Install | +100 |
From 0 Rates | 0 |
Category | Entertainment |
Size | 9 MB |
Last Update | 2021 August 21 |
Install | +100 |
From 0 Rates | 0 |
Category | Entertainment |
Size | 9 MB |
Last Update | 2021 August 21 |
Dangane Da Mu
Nahiyar Afirka akwai dama da yawa a cikinta a bangarori daban-daban. Tashar Hausa rediyo da talabijin wata hanya ce da ke hada alaka tsakanin Iran da mutanen nahiyar Afirka.
Tashar Hausa TV ita ce tashar talabijin ta farko da aka bude a hukumance Iran a cikin 2019, domin bayyana abubuwa da suka shafi nahiyar Afirka, tana da shafukan yanar gizo a cikin harsunan Hausa, Ingilishi, da kuma Farisanci.
Sannan rediyon Hausa da ke karkashin tashar yana watsa shirye-shirye sau 3 a rana, da kuma shirye-shirye na talabijin tsawon sa’oi 6, wanda ake maimaita su a ranar.
Daga cikin muhimman manufofin tashar rediyo da talabijin na Hausa sun hada da fadada alakoki tsakanin mutanen Iran da kasashen Afirka, da kuma nuna abubuwa da dama da al’ummomin biyu za su iya cin gajiyar juna.
Yin fashain baki a kan batutuwa da dama da suka shafi siyasar Iran da ma duniya, suna daga cikin manufofin tashar.
Babbar manufar bude bangaren harshen Farisanci a tashar shi ne, kara wayar da kan Iraniyawa kan muhimmancin karfafa alakoki tare da kasashen nahiyar Afirka a dukkanin bangarori.